9 Mayu 2025 - 22:27
Source: ABNA24
Imam Ridha (As): “La’ilaha Illallahu Garkuwa Ta Ce, Dukkan Wanda Ya Shiga Cikin Garkuwa To Ya Aminta Daga Azabata.

Allah Ta’ala Ya na cewa: “La’ilaha Illahu garkuwa ta ce, dukkan wanda ya shiga cikin garkuwa toya aminta daga azabata. Yayin da ayarin ya soma tafiya sai ya kiramu da cewa: amma da sharuddanta’ kuma Ni ina da daga cikin sharuddanta”.

Yau ce ranar Maulidin Imam Rida (AS) mai albarka. Ina so in bayyana wasu batutuwa game da shi. Wannan Imam mai girma ya samu ragamar Imamanci a cikin mawuyacin hali. Saboda yanayin zalunci na zamanin Haruna Rashid, mahaifinsa mai girma bai iya bayyana imamancinsa ba a bayyane karara ba. Lokacin da mahaifinsa ya yi shahada, babu wanda ya san wane ne Imami na gaba. Bisa yadda a ka’idar da ‘yan Shi’a suke akai, bayan shahadar Imam to babban dan Imam, wato Ahmad bn Musa (AS) shi za zamo Imami. Bisa yadda wasu hadisai da suka zo wa ‘yan Shi’a, lallai ne Imam wajibi ne ya na da Da domin ya zama Imam na gaba. Imam Riza (AS) shi kuma alokacin bai haihu ba. A daya bangaren kuma wakilan Imam Kazim (AS) ba su yarda da Imam Ridha (AS) ba, sai suka wai Imam Musa bai rasu ba. Sun karyata imamancinsa ne don su wawushe dukiyar da ke hannunsu da Imam Musa As ya basu ajiya, kada su ba Imam Ridha (AS). Duk wannan ya haifar da yanayi mai wahala ga Imam Ridha (AS).

Amma wannan Imami mai girma ya yi kokari da dukkan zuciyarsa wajen ganin ya cika babban hadafin da dukkanin Imamai suke da yunkurin isarwa tun daga Imam Ali (a.s.) har zuwa Imam Rida (a.s.) wato dawo da matsayin Ahlul Baiti (a.s) a cikin mutane, wanda ya yi rauni matuka tun lokacin da halifanci ya kauce daga babbar hanya.

Imam Riza (a.s) ya kasance yana tabbatar da imamancinsa a duk wata dama da ya samu bayan da wasu daga mabiya suka zama waqfiyyah. Ali bn Hamza ya tambayi Imam cewa: Ga wa mahaifinka ya danka wa Imamanci? Ya ce: "Ga ni." Ya ce, ba ka tsoron Haruna? Ya ce: "Idan har zai iya cutar da ni, to ni ba Imami ba ne".

A lokacin da Mamun Abbasi ya kai shi birnin Maru na Iran da tilasta masa wajen ya karbi matsayin mai jiran gadonsa wato yarimansa, Imam (a.s.) ya yi amfani da wannan dama da ya samu wajen yada da fayyace makirce-makircen Ma’amun da kuma bayyana hakikanin sakon musulunci. In da aka gudanar da muhawarori da dama, kuma cikin sauki ya yi nasara a kan manyan Kiristoci da Yahudawa da sauran addinai ta hanyar amfani da littattafansu da kuma tabbatar da gaskiyar Musulunci. Ta hanyar nuna iliminsa, ya sa dukkan mutane suka fahimci wanene ya cancanci halifancin Annabi, har ta kai ga an tilasta wa Mamun ya shelanta Shi'anci da kare imaman Amirul Muminina Ali (a.s.). Daga karshe da Ma’amun ya ga cewa mutane da tsananin soyayyarsu ga Imam Riza (a.s.) za su iya yi masa juyin juya hali su hanbarar da mulkinsa, sai ya shahadantar da Imam (a.s.).

Imam Riza (AS) ya iya kafa Musulunci tsantsa, wato cikakken Musulunci, sharadinsa shi ne samuwar Imam ma'asumi a shugabancin gwamnati, da mayar da matsayin Ahlul Baiti (AS) a cikin mutane zuwa matsayinsa na asali ta hanyar ayyukan da ya yi, ciki har da sanannen Hadisin sarkar Zinariya wato Silsilatuz Zahbi.

نص حديث سلسلة الذهب

حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ مُوسَى بْنِ الْمُتَوَكِّلِ رَحِمَهُ اللَّهُ، قَالَ حَدَّثَنَا عَلِيُّ بْنُ إِبْرَاهِيمَ عَنْ أَبِيهِ عَنْ يُوسُفَ بْنِ عَقِيلٍ عَنْ إِسْحَاقَ بْنِ رَاهَوَيْهِ قَالَ: لَمَّا وَافَى أَبُو الْحَسَنِ الرِّضَا عليه السلام نَيْسَابُورَ وَ أَرَادَ أَنْ يَرْحَلَ مِنْهَا إِلَى الْمَأْمُونِ اجْتَمَعَ إِلَيْهِ أَصْحَابُ الْحَدِيثِ فَقَالُوا لَهُ: يَا ابْنَ رَسُولِ اللَّهِ تَرْحَلُ عَنَّا وَ لَا تُحَدِّثُنَا بِحَدِيثٍ فَنَسْتَفِيدَهُ مِنْكَ؟!

وَ قَدْ كَانَ قَعَدَ فِي الْعَمَّارِيَّةِ فَأَطْلَعَ رَأْسَهُ وَ قَالَ: "سَمِعْتُ أَبِي مُوسَى بْنَ جَعْفَرٍ يَقُولُ: سَمِعْتُ أَبِي جَعْفَرَ بْنَ مُحَمَّدٍ يَقُولُ: سَمِعْتُ أَبِي مُحَمَّدَ بْنَ عَلِيٍّ يَقُولُ: سَمِعْتُ أَبِي عَلِيَّ بْنَ الْحُسَيْنِ يَقُولُ: سَمِعْتُ أَبِي الْحُسَيْنَ بْنَ عَلِيٍّ يَقُولُ: سَمِعْتُ أَبِي أَمِيرَ الْمُؤْمِنِينَ عَلِيَّ بْنَ أَبِي طَالِبٍ عليه السلام يَقُولُ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه و آله يَقُولُ: سَمِعْتُ جَبْرَئِيلَ يَقُولُ: سَمِعْتُ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ حِصْنِي فَمَنْ دَخَلَ حِصْنِي أَمِنَ مِنْ عَذَابِي فَلَمَّا مَرَّتِ الرَّاحِلَةُ نَادَانَا بِشُرُوطِهَا وَ أَنَا مِنْ‏ شُرُوطِهَا".

Nassin Hadisin Sarkar Zinare

Muhammad bn Musa bn al-Mutawakkil, Allah ya yi masa rahama, ya ruwaito mana, ya ce: “Ali ibn Ibrahim ya ba mu labari daga babansa, daga Yusuf bn Aqil, daga Ishaq bn Rahawayh, ya ce: “Lokacin da Abul-Hasan al-Rida, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya isa birnin Nayshabur, yayin da yayi niyyyar ci gaba da tafiyarsa’ zuwa ga Ma’amun sai  mutane ma’abuta rauwaitar hadisi suka taru gare shi’ suka ce da shi: ya kai dan Manzon Allah zaka tafi ka barmu alahli kuma baka zantar da mu da wani hadisi ba da zamu fa’idant da shi ba daga gareka?.

Ya kasance yana zaune a cikin mazaunin sirdin abun hawansa, sai ya leko da kansa ya ce: “Na ji babana Musa bn Ja’afar yana cewa: “Na ji babana Ja’afar bn Muhammad yana cewa: “Na ji babana Muhammad bn Ali yana cewa: “Na ji babana Ali bn Husaini yana cewa: “Na ji babana Husain bn Ali yana cewa: “Na ji Babana, Amirul Muminina, yana cewa ya ji Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa ya na ce: Na ji Babana Amirul Muminina, Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Naji mala’aika Jibrilu yana cewa: naji Allah Ta’ala Ya na cewa: “La’ilaha Illahu garkuwa ta ce, dukkan wanda ya shiga cikin garkuwa toya aminta daga azabata. Yayin da ayarin ya soma tafiya sai ya kiramu da cewa: amma da sharuddanta’ kuma Ni ina da daga cikin sharuddanta”.

Your Comment

You are replying to: .
captcha